XtGem Forum catalog
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA QUR'ANI
.
Jerin Littafan Shi’a Na 1
Wallafar Prof. Umar Labdo (H)
.
(Kashi na daya)
.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
.
‘Yan Shi’a suna kudure cewa Alkur’ani mai girma wanda yake a hannun Musulmi a yau ba cikakke ba ne; domin, a ganinsu, Sahabbai da suka tattara Alkur’ani a zamanin Abubakar da Usman, Allah ya kara yarda a gare su, sun sauya abubuwa da dama a cikinsa ta hanyar yin kare-kare da rage-rage a cikin ayoyinsa.
.
Suka ce wai wannan Alkur’ani da muke karanta wa a yau babu abinda yake cikinsa daga abinda aka saukar ga Annabi (SAW) sai dan kadan.
,
‘Yan Shi’a suna zargin Sahabbai da sauya Littafin Allah, da canja ayoyinsa. Suka ce wai Sahabban sun yi haka ne ta hanyar debe ayoyi masu yawa da aka saukar wadanda suke tona asirinsu da kuma ayoyi da suke nuna falalar Ali binu Abi Dalib(RA) da zuri’arsa.
.
Abinda suke nufi da tona asirinsu, wai bayyana kafirci da munafuncin Sahabbai. Wal iyazu billahi!! Saboda haka a wurin ‘yan Shi’a, ayoyi da yawa dake cikin Alqur’ani ba maganar Allah ba ce, wannan ya sa suke zabar abinda ya dace da son zukatansu a cikin Alkur’ani, saura kuwa su yi burus da shi.
.
Wani babban malaminsu mai suna Hashim binu Sulaiman Albaharani yana fadi a cikin wani littafi nasa da ya rubuta a kan Tafsiri,
.
“Ka sani cewa a hakikanin gaskiya wacce babu kokwanto a cikinta, gwargwadon ruwayoyi mutawatirai, wannan Alkur’ani da yake hannunmu sauye-sauye sun faru a cikinsa bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) kuma wadanda suka tattara shi bayan Annabi sun debe kalmomi da ayoyi masu yawa daga cikinsa.”
,
zaka sami wannan a cikin littafin (ALBURHAN FI TAFSIRIL QUR'AN na Hashim Albaharani, 36)
.
Zamu cigaba insha Allah



AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA QUR'ANI
.
Jerin Littafan Shi’a Na 1
.
Wallafar Prof. Umar Labdo (H)
.
(Kashi na biyu)
.
[Cigaba daga inda muka tsaya]
.
A cikin littafin Alkafi, littafin da ya fi ko wanne inganci a wajen ‘yan Shi’a, an yi bayanin gwargwadon abinda aka debe daga cikin Alqur’ani.
.
Marubucin littafin, watau Muhammad binu Ya’akub Alkulaini, ya ce,
.
“An ruwaito daga Abu Abdullahi (watau Imamin Shi’a na shida) cewa Alkur’anin da Jibrilu ya zo da shi ga Muhammad (SAW) aya dubu goma sha bakwai (17,000) ne.
.
[Duba littafi ALKAFI na kulaini 2/634].
.
Wannan yana nufin ke nan cewa Kur’anin da yake hannunmu dan ragowa ne kawai; domin kuwa a bisa ga wannan ruwaya wadanda suka tattara littafin a bayan rasuwar Annabi (SAW) sun debe kimanin sulusi biyu na littafin.
.
Za mu tabbatar da haka idan muka lura da cewa Alkur’anin da yake hannunmu, wanda Musulmi suka sani a yau, ayoyinsa dubu shida da dari biyu da talatin da shida ne (6,236) kawai, kamar yadda malaman Sunna suka tabbatar.
.
[Duba Tafsirin Kathir, 1/7].
.
Akwai ruwayoyi masu yawa a cikin littafan malaman Shi’a da suke izna da su, wadanda suka tabbatar da wannan mugunyar akida tasu.
.
Wani malaminsu mai suna Ni’imatullahi Aljaza’iri da ya kididdige ruwayoyin ya tabbatar da cewa sun fi dubu biyu
.
[Duba Faslul Khidabi 248].
.
Saboda haka, ita akida ce wacce dukkan ‘yan Shi’a, ciki har da na Nijeriya, suka yarda da ita. Kuma idan ka ji suna musun ta, to takiyya ce kawai suke yi, watau munafunci da yaudara!!
.
Zamu cigaba insha Allah.



AKIDAR YAN SHI'A DANGANE DA QUR'ANI
.
Jerin Littafan Shi’a Na 1
Wallafar Prof. Umar Labdo (H)
.
Kashi na uku
.
[Cigaba daga inda muka tsaya]
.
Wani kasurgumin malamin Shi’a, mai suna Hussain binu Muhammad Annuri Aldabarsi, ya rubuta shirgegen littafi musamman don ya tabbatar da akidar ‘yan Shi’a cewa Alkur’anin nan da yake a hannunmu a yau ba cikakke ba ne, kuma akwai sauye-sauye, da kare-kare, da rage-rage, a cikinsa.
.
Littafin wanda ya sa wa suna FaslulKhidab fi Ithbati Tahrifi KitabiRabbil Arbab, (watau Yankakkiyar Magana A Kan Tabbatar Da Sauya Littafin Mamallakin Mamallaka), ya kunshi dubunnan ruwayoyi daga Imaman Shi’a da malamansu wadanda suke tabbatar da cewa wai wadan nan sauye-sauye, da kare-kare, da rage-rage Sahabbai, wadanda suka hada da Abubakar da Umar da Usman, Allah ya yarda da su baki daya, su ne suka zartar da su.
.
A cikin littafin har ila yau, an tabbatar da cewa malaman Shi’a kaf, magabatansu da na bayansu, sun hadu a kan wannan akida.
.
[Duba Faslul Khidab na Aldabarsi, 34].
.
‘Yan Shi’a suna da nasu Alkur’ani dabam, wanda suke kira Mushafu Fadima, watau Kundin Fadima.
A ganinsu,MushafuFadima shine Kur’ani na gaskiya wanda Imamansu suka gado shi daga Nana Fadima diyar Manzon Allah (SAW) da mijinta Ali binu Abi Dalib, Allah ya kara musu yarda.
.
Zamu cigaba insha Allah.






Koma Saman Shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 310726

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358